Ƙasashen Waje
Iran ta gargaɗi Isra’ila kan ci gaba da kai hari kan Falasɗinawa
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/10/Screenshot_20231018-063926_1.jpg)
Iran ta gargaɗi Isra’ila da cewa za ta iya kai harin riga-kafi cikin ‘yan sa’o’i masu zuwa’ idan har Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Hamas a Gaza.
Tun bayan da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar da harin ba-zata kan Isra’ila a ranar 8 ga watan Oktoba, inda ta kashe fararen hula fiye da dubu ɗaya tare da yin garkuwa da ɗaruruwan ‘yan Isra’ila, Isra’ila ta mayar da martani, inda ta kai hare-hare kan maɓoyar Hamas da ke Gaza tare da daƙile mai, abinci da ruwa, a daidai lokacin da Isra’ila ke shirin mamaye Gaza.
Iran a ranar Talata, 17 ga Oktoba ta yi gargaɗin cewa wakilan ƙasar da ke yammacin Asiya za su iya kai hare-hare kan Isra’ila “a cikin sa’o’i masu zuwa”.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da ganawar da ya yi da babban sakataren ƙungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah a baya-bayan nan, ministan harkokin wajen ƙasar Iran Hossein Amirabdollahian ya bayyana cewa: A cikin sa’o’i masu zuwa, duk wani mataki na turjiya kan gwamnatin sahyoniyawa abu ne mai yiwuwa.
KU KUMA KARANTA: Yaƙin Falasɗinawa da Isra’ila: An fara kwaso ’yan Najeriya da suke can
Shugabannin gwagwarmaya ba za su ƙyale gwamnatin sahyoniyawan ta yi duk abin da ta ga dama a Gaza ba, sannan ta koma wasu fagagen gwagwarmayar,” in ji Amirabdollahian.
Ministan na Iran ya ƙara da cewa ƙasarsa ba ta ba da umarni ba ga ƙungiyoyin da Iran ke marawa baya a duk faɗin yankin amma tana goyon bayansu.
Amirabdollahian ya kuma yi barazanar idan yaƙin ya faɗaɗa zuwa wasu fagagen, “zai canza taswirar Isra’ila.
Ƙasashen Waje
Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu
![Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/IMG-20240702-WA0041.jpg)
Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu
Daga Ibraheem El-Tafseer
Frane Selak ya kasance wanda ya fi kowa tsallake rijiya da baya a duniya.
A shekarar 1962 ya tsallake haɗarin jirgin ƙasa wanda mutane 17 suka mutu, a 1963 jirgi ya faɗi da shi kowa ya mutu sai shi kaɗai ko ƙwarzane bai yi ba.
A shekarar 1966 motar safa ta lume da su a rafi mutum huɗu sun mutu amma Frane bai samu ko ƙwarzane ba a yayin da a shekarar 1973 motarsa ta kama da wuta ya tsallake rijiya da baya, ya kuma tsallake haɗarin taho mu gama da mota ta yi da shi ya tsira ya kuma lashe yuro dubu ɗari takwas a Caca a shekarar 2003.
KU KUMA KARANTA: Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki
Ƙasashen Waje
Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza
![Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/5760.jpg)
Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza
Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin ƙaurace wasu yankuna masu yawan jama’a.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar
Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka hallaka mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, cewar wata majiyar lafiya da kuma ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinawa.
Ƙasashen Waje
Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC
![Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana - COPEC](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/06/20261902_0-387-5446-3067.jpeg)
Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Man Fetur a Ghana ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a samun ƙarin farashin man fetur a ƙasar a farkon watan Yulin 2024.
Ƙungiyar ta Chamber for Petroleum Consumers (COPEC) ta ce akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa farashin fetur da man dizel da gas zai ƙaru baki ɗaya a gidajen man da ke faɗin ƙasar, kamar yadda kamfanin watsa labarai na ƙasar Ghana ya ruwaito.
COPEC ɗin ta ce za a samu ƙarin farashin ne sakamakon yadda farashin Cedi ɗin a ƙasar ke ƙara karewa idan aka kwatanta da dalar Amurka.
COPEC ɗin ta yi hasashen cewa farashin man fetur ɗin wanda za a rinƙa sayarwa a gidan mai zai ƙaru da kashi 2.17 cikin 100, wanda hakan ke nufin zai ƙaru daga Cedi 14.17 zuwa Cedi 15.20 a duk lita.
Sai kuma farashin dizel ana sa ran ya ƙaru zuwa 15.21 a kowace lita ɗaya, sai kuma na gas ya koma tsakanin Cedi 13.24 zuwa Cedi 14.64 a duk kilo ɗaya.
KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya
Ƙungiyar ta COPEC ta bayar da shawara ga gwamnatin Ghana da ta yi duk mai yiwuwa domin rage harajin da yake a kan gas ko kuma yin tallafi a farashinsa domin bayar da dama ga ‘yan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.
Ta kuma yi ƙira ga gwamnati da kada ta yi ƙasa a gwiwa wajen dawo da matatar mai ta Tema a kan aiki (TOR) don kaucewa ko kuma rage shigo tattacen man fetur wanda a wani lokacin ake samun gurɓatacce.
-
Kotu1 year ago
Kotu tayi watsi da ƙarar APC game da zaɓen Abba Gida Gida
-
Labarai9 months ago
Dalilin da ya sa na saka wa matata sasari – Wani magidanci a Potiskum
-
Ƙasashen Waje1 year ago
Ɗaliban Najeriya a Sudan sun nemi a kwaso su daga ƙasar
-
Labarai1 year ago
‘Yan banga sun kama wani mutum da ke yunƙurin sace yarinya a Kano