Injin niƙa ya gutsire kan wata mata a Kaduna

0
326
Injin niƙa ya gutsire kan wata mata a Kaduna

Injin niƙa ya gutsire kan wata mata a Kaduna

Daga Idris Umar, Zariya

Wani mummunan lamari mai cike da alhini ya faru a garin Mele da ke cikin ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna, inda wata mata mai suna Malama Hauwa Suleman ta rasa ranta yayin da injin niƙa ya kama hijabinta har ya janyo ta ya yanke mata wuya.

Lamarin ya faru a cikin wannan mako ne, lokacin da Malama Hauwa ta tafi garin Saminaka domin a surfa mata shinkafa don amfanin iyalinta. A cewar ɗanta, Inuwa Muhammad, mahaifiyarsu ta fita daga gida da nufin ta yi surfe, sai dai gawarta ce kawai aka dawo da ita gida.

“Ina tabbatar muku da cewa mahaifiyata ta rasu sakamakon wannan hadari da ya faru a wajen surfe shinkafa. Ta fita lafiya amma sai gawanta aka dawo mana da ita,” in ji Inuwa cikin kuka.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan shigarta wajen niƙa, ta duƙa domin ɗibar masarar da ke ƙasa. A yayin hakan ne iska ya daga hijabinta zuwa ga Bel ɗin Inji niƙan nan take Injin ɗin ya daure ta tam kuma ya gutsire mata wuya yayin da mai lura da Injin yarone kuma ganin lamarin duk ya rikece har Malama Hauwa ta cika.

Mijin mamaciyar, Malam Suleman Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilan manema labarai, tare da bayyana damuwarsa da jimaminsa game da abinda ya faru.

Ƙaninta, Malam Ishak Muhammad, ya bayyana cewa Malama Hauwa ta bar yara da dama, inda ya roki Allah ya jikan ta da rahama.

KU KUMA KARANTA: Jigo a Siyasar Jihar Kano ya rasu sanadiyyar hatsarin mota

Wani matashi mai suna Haruna Muhammad mazaunin garin Saminaka da wakilinmu ya zanta da shi, akan lamarin ya bayyana matuƙar damuwa bisa yadda mata da yara ke zuwa irin waɗannan wurare ba tare da kula da haɗarin da ke tattare da su ba. Ya bukaci gwamnati da shugabannin al’umma su ɗauki matakan kare rayuka ta hanyar wayar da kai da kuma ɗaura dokoki kan amfanin injinan aikin hannu.

An yi jana’izar Malama Hauwa a garin Mele, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Shawarwari Ga Jama’a

Kada a je wuraren niƙa da dogayen hijabi ko tufafi masu yawan yawo.

A tabbatar da tsaron injinan aiki tare da wayar da kan masu amfani da su.

A guji aiken ƙanana ko mata marasa ƙarfi zuwa wuraren da ke da haɗari.

Leave a Reply