INEC ta shirya zaɓen Adamawa da Kebbi a watan gobe

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana ranar da za a sake gudanar da zaɓukan jihohin Kebbi da Adamawa.

Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi, babban sakataren yaɗa labarai na shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a Abuja, a ranar Litinin.

Ya ce za a gudanar da zaɓukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a rana guda.

“Hakan ya taso ne daga taron da ta gudanar a yau, INEC ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkan zaɓukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a ranar Asabar 15 ga Afrilu, 2023,” in ji Oyekanmi.

KU KUMA KARANTA: Anyi inkwankulusib a zaɓen Adamawa

Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da cikakken bayani a hukumance.

Zaɓukan shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma na gwamnoni da na majalisun jihohi na ranar 18 ga Maris sun shaida soke zaɓen da wasu zaɓukan da ba a kammala ba a faɗin kasar nan ba, waɗanda sune INEC ta bada sanarwar za ayi su a watan gobe.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *