INEC ta samu ƙarin jam’iyyu 7 dake neman a yi musu rajista
Daga Jameel Lawan Yakasai
Wata sanarwa da INEC ta fitar ta ce, a cikin mako guda an samu ƙarin ƙungiyoyi 7, da ke son a yi musu rajistar zama jam’iyyun siyasa.
A cewar INEC yanzu haka adadin masu neman a yi musu rijistar ya kai 129.
KU KUMA KARANTA: INEC ta sanya ranar 16 ga Agusta don zaɓen cike gurbi a mazabu 16
INEC ta ƙara da cewa yanzu haka shirye shirye sun yi nisa wajen samar da shafin intanet, wanda za a yi amfani da shi wajen yin rijistar jam’iyyun.









