Indai sahihin zaɓe za a yi NNPP za ta kayar da APC da PDP – Kwankwaso
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Sanata Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce jam’iyyar NNPP za ta kayar da dukkan jam’iyyun siyasa a zaɓe mai inganci da adalci.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar a Abuja.
Dan takarar NNPP a zaben 2023 din ya soki gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa ‘yan Najeriya na fuskantar matsin rayuwa fiye da yadda aka taba gani a baya.
KU KUMA KARANTA:Kotu ta aikewa Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sammaci bisa zargin ɓatanci ga gwamnan Kano
“Gaskiya ne da wuya a tuna da wani da ke farin ciki da gwamnatin APC a kowane mataki, musamman a matakin tarayya,” in ji shi.
“‘Yan Najeriya sun shaida wahalhalu da ba a taba gani ba a tarihin wannan kasa.
“Talauci ya yadu ko’ina. Mun ga rashin tsaro, gine-gine da ababen more rayuwa suna lalacewa, kuma ba mu ga wani kokari na gyara su ba.
“Na yi imani idan aka gudanar da sahihin zabe a wannan kasa, jam’iyyarmu za ta kayar da APC, PDP da sauran jam’iyyu.”