Ina neman diyyar mahaifina – Ɗan Mai Tsaron Sarkin Kano Sanusi da aka kashe

0
31
Ina neman diyyar mahaifina - Ɗan Mai Tsaron Sarkin Kano Sanusi da aka kashe

Ina neman diyyar mahaifina – Ɗan Mai Tsaron Sarkin Kano Sanusi da aka kashe

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Mahaifin Surajo Rabiu, ɗaya daga cikin ‘yan banga na unguwar Jaɓa a ƙaramar hukumar Fagge dake Jihar Kano, ya bukaci a bi masa hakkin dansa tare da biyan diyya bayan kisan da aka yi masa a cikin tawagar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, bayan sallar Idi.

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai, mahaifin mamacin Malam Muhammadu Rabiu, ya bayyana yadda lamarin ya faru har ya kai ga mutuwar dansa.

Ya ce Surajo ya fara yanke shawarar kin halartar sallar Idi, inda ya ci gaba da aikin gyaran na’urorin lantarki. Amma daga bisani ya canja ra’ayi, ya sanya kayan aikinsa na bijilanti, sannan ya fita zuwa wurin sallar.

Marigayi Surajo, ya rasu yana da shekaru 26 a rayuwa, shi ne na hudu a cikin ‘ya’yan Malam Muhammadu Rabi’u goma sha biyu 12. Mahaifinsa ya bayyana marigayin a matsayin matashi mai biyayya da hakuri. “Dansu ya sadaukar da kansa don tsaron al’umma,” a cewar sa. “Yana aiki ne a matsayin mai tsaro don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, amma aka kashe shi yana bakin aiki.”

KU KUMA KARANTA:A tabbata an bi haƙƙin waɗanda aka kashe a Edo, an kuma biya su diyya – Gwamnan Kano

Mahaifin marigayin ya bukaci gwamnatin Jihar Kano da Masarautar Kano da su tabbatar da gudanar da bincike sahihi, sannan ayi adalci domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da biyan diyya ga iyalansa.

“Surajo matashi ne mai tarbiyya da mutunci. Bai taba shan taba ba, balle ya yi hulda da mugayen mutane. Makwabtanmu za su iya tabbatar da hakan,” in ji mahaifin marigayin.

Bayan wannan mummunan hari da aka kai wa ‘yan bijilanti a tawagar Sarkin Kano a ranar Lahadi, 30 ga watan Maris, jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike. A halin yanzu, Malam Muhammadu Rabi’u tare da shugabannin kungiyar ‘yan bijilanti suna kokarin ganin an yi adalci kan kisan Surajo.

Leave a Reply