Ina kira ga ‘yan kasuwar Potiskum da su zo mu haɗa kai mu ciyar da wannan kamfani gaba – Babban Manajan Yobe Flour

0
577
Ina kira ga 'yan kasuwar Potiskum da su zo mu haɗa kai mu ciyar da wannan kamfani gaba - Babban Manajan Yobe Flour
Alhaji Saminu Utai, babban manajan kamfanin Yobe Flour Mills

Ina kira ga ‘yan kasuwar Potiskum da su zo mu haɗa kai mu ciyar da wannan kamfani gaba – Babban Manajan Yobe Flour

Babban manajan kamfanin ‘Yobe Flour and Feed Mills’ da ke Potiskum, Alhaji Saminu Utai (Turaki Bai of Fika) ne ya bayyana haka a tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Neptune Prime. Kamfanin Yobe Flour, kamfani ne da ya daɗe yana aikin sarrafa kayan abinci iri daban-daban a jihar Yobe.

Babban manajan, ya shaidawa Neptune Prime cewa “ayyukan da muke yi a wannan kamfani sun haɗa da Fulawa, Biskin Masara, Garin Laushi da Dusar dabbobi. Kullum muke gudanar da aikin mu, idan ka ga ba mu yi aiki ba, to Janareto ne ya ba mu matsala. Don wani lokacin ma, masu saya har jiranmu suke yi”

Ya ci gaba da cewa ” A ƙoƙarin Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, na farfaɗo da duk kamfanonin da ba sa aiki a jihar, to wannan kamfani na ɗaya daga cikin waɗanda suka farfaɗo. Da yake wannan kamfani ya daɗe ba ya aiki, sai da na zo ni. Wato bayan an naɗa ni babban manajan wannan kamfani, yanzu haka wannan kamfani yana aiki a kullum. Wani lokacin har dare muke kaiwa muna aiki a wannan kamfani.

Sannan muna tura kaya a Damaturu, Gaidam, Gashuwa, da Nguru. Sannan muna fitar da kaya Maiduguri da Kano.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya yabawa Gwamnan Yobe kan bunƙasa harkar noma a jihar

Potiskum ita ce cibiyar kasuwancin jihar Yobe, da wannan nake kira ga ‘yan kasuwar garin Potiskum da su zo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu ciyar da wannan kamfani gaba. Saboda hakan zai taimake mu, zai taimaki jihar Yobe baki ɗaya. Akwai mutane da yawa da ba su da ayyukan yi, idan har suka zo, muka haɗu da mu da su, muka girmar da wannan kamfani, to mutane da dama za su samu abin yi. Kuma za a rage masu zaman banza. Inji shi.

Utai ya ƙara da cewa “Babbar matsalar kamfani shi ne jari, to muna godewa Allah, mun samu goyon baya daga gwamnatin jihar Yobe. Mun samu jari wanda muke yin aiki a kullum. Ba mu da matsalar jari. Sai dai batun matsalar kwastomomi. Kasantuwar daina aiki da kamfanin ya yi na tsawon lokaci, to hakan ya sa mun rasa wasu kwastomominmu, amma yanzu muna binsu, muna shaida musu cewa, kamfani ya dawo aiki fiye da yadda yake aiki a shekarun baya.

Kuma kwastomomin sun zo sun duba kayan, sun ga kayan yana da kyau fiye da wanda suke sayar wa a shagunansu. A watannin baya da ‘yan kasuwar Potiskum ba sa sayan kayan mu sosai, amma yanzu ganin cewa kayan ya fi wanda suke sayar wa a shagunansu kyau, to yanzu kam suna zuwa su sayi kayan sosai.

Da yake Gwamnan Yobe yana so wannan kamfani ya bunƙasa fiye da yadda yake a yanzu, to akwai shawarwari da yake ba mu don inganta wannan aiki da ci gaban wannan kamfani”. Inji Babban manajan.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya biya bashin Naira biliyan 39, ya jaddada tsare-tsaren tattalin arziƙi

Tun da farko, Alhaji Saminu Utai (Turaki Bai na Fika) ya fara da bayyana taƙaitaccen tarihinsa. Inda ya fara da cewa “An haife ni a garin Potiskum. Na yi Firamare na a central. Na yi da Sakandire na a Fika GSS Potiskum. Sannan na wuce Federal Polytechnic Bauchi na yi Diploma. Na wuce jami’ar Maiduguri inda na yi Digiri a fannin kasuwanci. Na yi hidimar ƙasa a jihar Kaduna, kamfanin ba da wutar lantarki ta ƙasa (Power Holding Company of Nigeria).

Kafin Gwamna Mai Mala Buni ya naɗa ni a matsayin babban manajan Yobe Flour, ina aiki ne a ma’aikatar ‘Federal Character Commission’ a jihar Yobe.

Leave a Reply