No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ina ƙira ga ‘yan Najeriya a ƙara haƙuri da Tinubu – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya roki ‘yan Najeriya su kara hakuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu game da sauye-sauyen da yake aiwatarwa wadanda suka haddasawa mutane da dama kuncin rayuwa.

Ganduje ya bayyana hakan ne a sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Edwin Olofu ya fitar yayin shagulgulan bikin kirsimeti na bana.

Yana hawan kan karagar mulki a 2023, shugaban kasar ya sanar da bullo da wasu muhimman manufofi guda 2 na janye tallafin man fetur da kuma hade harkar musayar kudade a wuri guda.

Nan da nan wadannan manufofi suka sabbaba hauhawar farashin da ba a taba ganin irinta ba a kasar, al’amarin da ya jefa dimbin ‘yan Najeriya cikin halin ni ‘ya su har ta kai ga da kyar suke iya ci da kansu.

Sai dai, a yayin da sakon tsohon gwamnan jihar Kanon ke kira da a kara hakuri, yace an fara tasirin sauye-sauyen gwamnatin Tinubun.

Ya kuma ba da tabbacin cewa kan nan da bikin kirsimetin badi, tattalin arzikin Najeriya zai kara daidaita, inda yace kokarin gwamnatin na samar da tsaro a fadin kasar ya fara haifar da da-mai ido kasancewar an samu matukar raguwar matsalolin ‘yan bindiga da yin garkuwa da mutane.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...