Shugaban mulkin sojin Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya hau kan mulki bayan mutuwar mahaifinsa a 2021, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen da za a yi a watan Mayu mai zuwa.
Mahamat Idriss Deby ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya ranar Asabar a N’Djamena, babban birnin ƙasar.
“Ni, Mahamat Idriss Deby Itno, ne ɗan takarar shugaban ƙasa na gamayyar jam’iyyun United Chad coalition a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024,” in ji shi.
Hukumar zaɓen ƙasar ta ce za a gudanar da zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa ranar 6 ga watan Mayu mai zuwa.
KU KUMA KARANTA: Ƙasar Chadi ta sanar da ranar zaɓe don komawa tafarkin Dimokuraɗiyya
A tsakiyar watan Janairun da ya gabata, jam’iyyar Patriotic Salvation Movement (MPS) ta ayyana Mahamat Deby Itno a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa.
Deby Itno ya hau kan mulki ne a shekarar 2021 bayan mahaifinsa Idriss Deby Itno, wanda ya kwashe kusan shekara talatin a kan mulki, ya mutu a fagen yaƙi yayin fafatawa da wasu ƴan tawayen ƙasar.