“Idan na saɓa rantsuwar da na yi, babu lauyan da zai kare ni a cikin kabari” – Gwamnan Kano

2
455

Daga Shafa’atu Dauda, Kano

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa idan yana cikin kabari babu wani Lauya da zai iya kare shi a wajen Allah idan ya saɓa rantsuwar da ya yi da Alƙur’ani.

Gwamna Abba yace ɓarnar da tsohon Gwamnan Jihar Kano ya yi a jihar, ta wuce misali, sai wanda ya gani da idonsa ne zai tabbatar da hakan.

Ya ƙara da cewa abin mamaki shi ne, yadda tsohon Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje ya mallaka wa iyalansa manyan kadarorin gwamnatin jihar.

Zamu wallafa jerin sunayen waɗanda aka bawa muhimman wuraren da al’ummar jihar Kano ke amfana dasu saboda son zuciya a cewar Gwamna Abba Kabir.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano Abba, ya naɗa mataimaka 14

Ya kawo misali da Daula Hotel wanda ya bayyana sunan Hajiya Balaraba Ganduje da mijinta wanda kuma shi ne shugaban hukumar tsara birane ta jihar Kano (KNUPDA).

Yana mai cewa kuma kamfanin da ya yi aikin ginin Daula Hotel mallakin ‘yar Ganduje ce da kuma surikinsa. Inji Abba Kabir Yusuf

Dan haka yace ya yi rantsuwa da Alƙur’ani cewa zai yi aiki tsakaninsa da Allah kuma Allah zai tambaye shi idan ya koma gare Shi.

2 COMMENTS

Leave a Reply