Hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijar OCRTIS ta ce a 2022 jami’anta sun kama miyagun ƙwayoyi da kuɗaɗensu suka kai biliyan 26.
A sanarwar da kakakin hukumar ‘yan sanda ta Nijar, Kwamishina Habou Mountari ya fitar, hukumar ta OCRTIS ta kama mutum 5,532 da take zargi da safarar miyagun kwayoyi.
A cewar sanarwar, mutum 210 a cikinsu mata ne sai kuma 454 ‘yan ƙasashen waje.
Sanarwar ta ce ƙasar ta Nijar ta kasance tamkar wata hanya da masu safarar miyagun ƙwayoyin ke amfani da ita wurin jigila zuwa ƙasashen Libiya da Aljeriya har zuwa ƙasashen Turai.
Hukumar ta ƙara da cewa kaso 5.62 na waɗanda aka kama shekarunsu ba su haura 18 ba sai kashi 58.92 sun kama daga 18 ne zuwa 29.
Hukumar ta ce tana yin iya bakin kokarinta domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyin, sai dai masu safarar suna fito da sabbin dabaru a kullum na kauce wa shingayen bincikensu.