Hukumar ƙidaya ta ƙasa, ta bayyana dalilin ɗage ranar ƙidaya a ƙasar

Hukumar ƙidaya ta ƙasa, (NPC), ta ce an ɗage ƙidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 ne saboda shirin miƙa mulki na gwamnati da kuma yanayin da ƙasar ke ciki bayan zaɓe.

Inuwa Jalingo, manajan ƙidaya na shekarar 2023 kuma darakta, hukumar ƙidaya ta ƙasa NPC, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi.

Jalingo wanda ya tabbatar da shirin hukumar na ƙidayar jama’a a shekarar 2023, ya ce NPC ta shirya yin ƙidayar jama’a na farko a Najeriya.

Ya ce hukumar ta samu nasara mafi girma a dukkan fannoni ta fuskar shirye-shiryen.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗage ƙidayar jama’a

“Mun cimma daidaiton ƙasashen duniya don ƙidayar cikin tsari. “Kimanin na’urori na na zamani guda 450,000 an sayo kuma an rarraba su ga dukkan ƙananan hukumomi,” in ji shi.

Mista Jalingo ya ce duk da haka, gwamnati na ci gaba da aiki, yana mai fatan gwamnatin mai jiran gado za ta ci gaba da samun nasarorin da aka samu domin gudanar da ƙidayar.

Manajan ƙidayar ya yabawa gwamnatin Buhari bisa goyon bayan da ta bayar, inda ya ce hukumar ta samu nasarar horar da malamai kusan 60,000 a faɗin kasar nan.

“Duk wanda ya ce ba mu shirya ba dole ne ya faɗi haka cikin jahilci,” in ji shi. Mista Jalingo ya nanata fa’idar ƙidayar jama’a da ba ta rasa nasaba da tsare-tsare na tattalin arziƙin ƙasa da samar da bayanan tsare-tsare na gudanarwa.

Ya ce hukumar ta iya tattara ‘yan Najeriya domin a yi ƙidayar da duk wani bayani da ake buƙata domin a samu nasarar ƙidayar jama’a.

Hukumar NPC ta ɗage ƙidayar yawan jama’a da gidaje da aka shirya tun daga ranar 3 ga Mayu zuwa 7 ga Mayu.


Comments

One response to “Hukumar ƙidaya ta ƙasa, ta bayyana dalilin ɗage ranar ƙidaya a ƙasar”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Hukumar ƙidaya ta ƙasa, ta bayyana dalilin ɗage ranar ƙidaya a ƙasar […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *