Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin fim ko waƙa
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar tace fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta bayyana matsayarta, kan korafe-korafen da al’umma suka shigar gabanta, tare da wasu malamai a Jihar, kan Usman da aka sani da Sojaboy, dangane da wani sabon salon waƙa da yake ƙoƙarin fitowa da shi, wanda ya saɓa da koyarwar addinin musulunci tare da al’adar malam bahaushe.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya amince da ƙwace lasisin mawaƙin Sojaboy da Shamsiyya Muhammad tare da Hasana Suzan ya yin, sanarwar ta buƙaci masu gidajen wasanni tare duk wani wanda yake mu’amalar aiki dasu da ya yi biyayya ga wannan matakin na hukumar domin cigaban Jihar Kano.
Abba El-mustapha ya baiwa sashin tace fina-finai na Hukumar umarnin cewa daga wannan lokacin kada a ƙara tace duk wani fim da aka hangi fuskokinsu a ciki, tare da ƙira ga masu shirya fina-finai musamman daraktoci da su kiyayi yin duk wata hulɗar aiki dasu domin gujewa fishin Hukumar.
KU KUMA KARANTA: Hukumar tace fina-finai a Kano ta dakatar da jaruma Samha M Inuwa
Kafin ta dauki irin wannan matakin Hukumar na yin iya ƙoƙarinta kan gargaɗar masu irin wannan halayya da su ƙiyayi yin duk wani abu da zai zubar da kimarsu ko sana’arsu.
Inda ta kara jaddada cewa bazata dauki duk wani abu da zai taba addini, al’ada ko tarbiyar a’lummar Jihar Kano da sauki ba.
Haka kuma, bazata goyi bayan ire-iren wannan halayyar ba da sunan sana’a a Jihar ba.
Idan ba’a manta ba a watan da ya gabata ne Hukumar ta dauki irin wannan mataki ga daya daga cikin fitattun jarumai a Masana’antar ta kannywood wato Samha M Inuwa, da nufin tsaftace Masana’antar tare da tabbatar da kowa nabin dokokin Hukumar sau da kafa.