Hukumar tace fina-finai a Kano ta dakatar da jaruma Samha M Inuwa
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano ta dakatar da jaruma Samha M Inuwa daga shiga harkar fim na tsawon shekara ɗaya, tare da ƙwace shedarta ta zama halastacciyar ‘yar film.
A wata sanarwar da jami’in yaɗa labaran Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aika wa manema labarai ya shaida cewa Hukumar ta sha alwashin ƙin ƙara tace duk wani fim da Samha ɗin ta fito a ciki.
KU KUMA KARANTA:Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Slow rasuwa
Wannan ya biyo bayan wasu ƙorafe-ƙorafe da al’umma suka yi kan wani bidiyo da jarumar ta saki dake nuna shigar da ba ta dace da koyarwar addinin musulunci ba, ba ya ga samunta da yin kalaman da ba su dace ba.
Ya zuwa yanzu dai hukumar ta dakatar da Samha har tsawon shekara ɗaya a wani mataki na tabbatar da bin dokokin Hukumar tare da ƙara tsaftace Masana’antar kannywood.