No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta dakatar da Mai Shari’a S.O Falola na Babbar Kotun Jihar Osun tare da neman a yi masa ritayar dole kan laifin saɓa ƙa’idar aiki da kuma bayar da umarnin kotu ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar NJC ta kuma kafa kwamitoci 11 domin bincike kan wasu alkalai 51 da ta samu takardun ƙorafi a kansu.

Sakataren yaɗa labaran NUJC Soji Oye ya ce an dakatar da Falola ne sai abin da hali ya yi, a yayin da take jiran abin da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, zai yi kan shawarar ritayar dolen.

Soji Oye ya ce NJC a taronta na 104 a Abuja, ta samu Mai Shari’a S.O. Falola da lafin ba da umarnin biyan N283,174,000 ga Bankin Polaris da wata buƙuwar hanya.

An gano laifin nasa ne bayan takardar ƙorafin da Bankin Polaris da wani mai suna Dapo Kolapo Olowo suka aike wa NJC kan lamarin.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta yanke wa sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami hukuncin kisa

An same shi da laifin ba da umarnin cire kuɗaɗen daga asusun bankin masu ƙara maimakon asusun wanda ake ƙara — ainihin waɗanda umarnin ya shafa.

An kuma samu Jastis Falola da laifin sauraron shari’a mai lamba HIK/41/2018, wadda ba shi da hurumi a kai, ba tare da ya samun takardar hukuncin daga Babbar Kotun Jihar Kwara ba, kuma ba tare da takardar shaidar rajistar shari’ar a Jihar Osun ba — inda yake da hurumi.

Soji Oye ya ce a taron NJC karo na 104 a Abuja, karkashin jagorancin Shugaban Alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya yi watsi da buƙatar Gwamna Adeleke na neman rantsar da muƙaddashin babban alkalin jihar.

Gwamnan ya nemi amincewar NJC ne bayan samun korafi kan Babban Alkalin jihar, Oyebola Adepele-Ojo da kuma matsayar da majalisar jihar ta cimma na dakatar da shi.

Soji Oye ya ce a taron NJC, ta kafa kwamitoci 11 domin bincikar alkalai 51 da ta samu korafi a kansu.

Amma kuma, bisa rahoton kwamitocin binciken wasu alkalai da ta kafa a baya, ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da aka shigar kan wasu alkalai saboda rashin hujjoji ko janyewar masu korafin.

Alkalan da aka wanke su ne Babban Alkalin Jihar Akwa Ibom, Jastis Ekaete F. F. Obot; Jastis Benson Anya na Babbar Kotun Jihar Abia; Jastis Z. B. Abubakar na Babbar Kotun Tarayya; Jastis Opufaa Ben-Whyte da kuma Augusta Uche K. Chuku na Babbar Kotun Jihar Ribas.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...