Hukumar NYSC ta haɗa kai da jami’an tsaro domin ƙubutar da ‘yan hidimar ƙasa da aka sace a Zamfara

Hukumar NYSC ta ce tana aiki tare da jami’an tsaro domin ganin an sako wasu ‘yan masu yi wa ƙasa hidima guda takwas, waɗanda aka yi garkuwa da su a Zamfara a kan hanyarsu ta zuwa sansanin horon da su da ke Sakkwato.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NYSC, Eddy Megwa, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarta cewa, ya naƙalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NYSC babban daraktan hukumar NYSC Yusha’u Ahmed ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin wani zaman tattaunawa da mambobin kwamitin majalisar wakilai kan matasa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Bindiga a Zamfara, sun buƙaci miliyan huɗu ga ‘yar NYSC da suka sace

Sanarwar ta ce, hukumar gudanarwar shirin tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki daban-daban da suka haɗa da gwamnatin Zamfara, sarakunan gargajiya, malamai da dai sauransu, domin ganin an sako mutanen da aka sace ba tare da wani rauni ba.

Birgediya-janar Ahmed, ya kuma gabatar da cikakken rahoto mai ɗauke da shaida na hoto na ziyarar da ya kai ga masu ruwa da tsaki a Zamfara, lamarin da ke nuni da cewa shirin ya ba da fifiko kan tsaro da jin daɗin dukkanin jami’an ƙungiyar.

Shugaban Kwamitin Matasa na Majalisar, Martin Esin, a nasa jawabin, ya yaba wa DG bisa girmama gayyatar kwamitin da kuma irin namijin ƙoƙarin da ya yi na ganin ‘yan ƙungiyar da aka sace sun samu ‘yanci.

Mista Esin ya yi alƙawarin goyon bayan kwamitin kan duk wani lamari na majalisa da zai ba da damar shirin ya ƙarfafa kan nasarorin da ya samu a lokacin jubili.

Ya kuma yaba wa Ahmed bisa ƙoƙarin da shirin ya yi na sake buɗe sansanin ‘yan hidimar ƙasa na jihar Borno bayan an daɗe da rufe shi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *