Hukumar NYSC ta biya diyya ga dangin ɗan bautar ƙasa da ya ɓata

2
387

Hukumar kula matasa masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) ta biya kuɗin inshora ga dangin wani ɗan bautar ƙasa mai suna Omale Victor mai lambar jihar EB/21A/1487, wanda ya ɓace a shekarar 2021, a lokacin da ya yi aiki hidimar ƙasa a jihar Ebonyi.

Victor, mai shekaru 24 a lokacin, an bayyana ɓacewarsa ne a ranar 9 ga watan Nuwamban 2021, ta hannun mai ɗakinsa Innocent Ujah, wanda ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa Victor ya bar gidansa da misalin ƙarfe 6 na yammacin wannan rana, kuma bai dawo ba.

Kafin batarsa, Victor yana aiki ne a hukumar kula da karatun jama’a ta jihar Ebonyi dake kan tsohuwar titin Enugu/Abakaliki ta cocin Presbyterian Church Kpirikpiri, Abakaliki, a babban birnin jihar.

KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun kashe ɗan bautar ƙasa, bayan karɓar kuɗin fansa

Darakta-Janar na NYSC na lokacin da sauran jami’an hukumar sun ziyarci iyalan Omale a Lokoja a shekarar 2021 lokacin da lamarin ya faru.

Tuni dai iyalan suka tuntuɓi mahukuntan hukumar NYSC.

Shugaban masu yi wa kasa hidima, NYSC, Birgediya Janar Ahmed, a lokacin da yake mika cekin kuɗin ga iyayen marigayin, Mista Samuel da Mrs Elizabeth Omale a gidansu da ke Lokoja, a ranar Alhamis, ya ce shirin zai ci gaba da tantance dangin.

Ya kuma ja hankalin ‘yan uwa da kar su yi rauni da imani da Allah, ya ƙara da cewa hukumar NYSC za ta ci gaba da nuna ƙauna da jajircewa a gare su.

Dangin Omale sun godewa hukumar NYSC bisa yadda suka kyautata ma iyalansa tun faruwar lamarin, sun kuma yi addu’ar Allah ya dawo da dansu da ransa.

Shugaban ya samu rakiyar Daraktan ayyuka na musamman Alhaji Musa Abubakar; Daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a Mista Eddy Megwa; Darakta, Sabis na Kula da Lafiya; Mista Ayodele Omotade; da kuma Kodinetan NYSC na jihar Kogi, Mrs Mofoluwaso Williams.

2 COMMENTS

Leave a Reply