Hukumar NSCDC ta kama mutane 6 da ake zargi da lalata wutar Lantarki a Jihar Kano

0
120
Hukumar NSCDC ta kama mutane 6 da ake zargi da lalata wutar Lantarki a Jihar Kano

Hukumar NSCDC ta kama mutane 6 da ake zargi da lalata wutar Lantarki a Jihar Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) a Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi da sata da lalata kayan wutar lantarki a unguwar Hayin Da’e da Hotoro da ke yankin ƙaramar hukumar Tarauni.

Sanarwar da kakakin hukumar a kano SC Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar a ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025.

Sanarwar ta ce an kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri daga yan sa kai a yankin, inda aka cafke su da wayoyin lantarki da suka cire daga kan wata transformer cikin dare.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NSCDC ta kama mutane 7 da ake zargi da sace murafan kwalbati

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Muhammad Yusuf mai shekara 18, Muhd Sani Adamu 19, Umar Musa 19, Ahmed Auwal 20, Muhd Yusuf 28 da kuma Usman Ali 19, waɗanda yawancinsu mazauna yankin ne.

NSCDC ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa waɗannan mutane sun dade suna addabar al’ummar Hayin Da’e, Farawa Kwanar Yashi da Hotoro ta hanyar fasa ƙofa, sata da kuma lalata kayan wutar lantarki.

Hukumar ta ce ta fara cikakken bincike, inda za a mika wadanda ake zargin kotu bayan kammala rahoto.

Leave a Reply