Hukumar NSCDC a Gombe ta kama mutane takwas kan zargin sayar da naman mushe

0
188

Hukumar tsaro ta ‘Nigerian Security and Civil Defence Corp’ (NSCDC) a jihar Gombe ta gabatar da wasu mutane takwas da ta kamo da ake zargin suna sayar wa mutane mushen nama.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai a hedkwatar hukumar, Kwamandanta na Jihar Gombe, Muhammad Bello Mu’azu, ya ce rundunar ta fara kama jagorar waɗanda ake zargin ce mai suna Mary Paul tare wasu mutum huɗu, kafin daga bisani ta sake kama wasu ƙarin mutum uku.

Kwamandan wanda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SC Buhari Sa’ad, ya yi magana a madadinsa ya ce sun kama mutanen ne bisa bayanan sirri da suka samu kan haramtacciyar sana’ar da ake zargin mutanen na yi.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NSCDC ta nemi haɗin kan ‘yan sanda akan rashin tsaro a Abuja

Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a wata kasuwar da ke a kwaryar cikin Gombe, kasancewar sun saba sayar da mushen ga jama’a a jihar da ma wasu jihohin Kudancin ƙasar nan, musamman Jihar Delta.

A cewar Kwamandan, Mary da tawagarta yawanci suna sarrafa naman ne tare da gyara shi don sayarwa jama’a ba tare da sun san naman mushe ba ne.

Ya kuma ce jami’ansa sun kama wasu ma a babur mai ƙafa uku ɗauke da wata matacciyar saniya da suka sayo daga Kanawa a yankin Ƙaramar hukumar Yamaltu Deba inda suka sa aka binne ta a wajen gari.

Muhammad Bello Mu’azu, yace da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Sannan sai ya ƙirayi jama’a da su yi hattara da irin naman da suke saya, da inda suke saya da kuma wurin waɗanda suke saya.

Jagorar waɗanda ake zargin, Mary Paul, ta ce a baya tana sayar da naman daji ne da aka farauto, amma dai daga baya ta koma sayar da mushen.

Mary ta ce ta shafe tsawon shekaru tana wannan sana’ar inda take amfani da sinadarai wajen sarrafa naman da kuma adana shi.

Leave a Reply