Hukumar NIMC ta gargaɗi ‘yan Najeriya da su daina sayar da lambar NIN ɗin su
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar NIMC ta gargadi ’yan Najeriya da su daina sayar da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) da sauran bayanan sirri kan kuɗin da bai haura (₦1,500 zuwa ₦2,000) ba, saboda hakan na barazana ga tsaron kasa da lafiyar Al’umma.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar EFCC ta gano cewa matasa da dama na sayar da bayanan mutane ga kamfanonin Fintech har ₦5,000.
EFCC ta kuma bayyana sabuwar hanyar damfara ta intanet inda masu zamba ke amfani da tallan tikitin jirgi na bogi da kuma manhajojin da ke dauke da cutarwa (malware) domin samun damar shiga asusun banki na mutane.
Har ila yau, an gano cewa akwai gungun masu damfara da ake kira “Account Suppliers” suna sayen bayanan NIN, BVN da hotuna daga mutane don bude asusun karya da yin damfara ta kudi.
NIMC da EFCC sun jaddada cewa irin waɗannan ayyuka na barazana ga tsaron kasa, kuma sun bukaci jama’a da su guji shiga irin wadannan halaye tare da kiyaye bayanan sirri na kansu.









