Hukumar NEMA ta rarraba kayayyakin agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa a Kaduna

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta fara raba kayan agaji ga waɗanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su da kuma sauran marasa galihu a jihar Kaduna bisa manufar bayar da agajin gaggawa na musamman na tattalin arziƙi da rayuwa (SNELEI).

Darakta Janar na Hukumar NEMA Mustapha Habib Ahmed wanda ya ƙaddamar da rabon kayayyakin a Kaduna a jiya, ya ce gwamnatin tarayya ta amince da ɗaukar matakin ne musamman ga mutanen da bala’in ambaliyan ruwa ya shafa a shekarar 2022 da kuma waɗanda aka bayyana a matsayin waɗanda suka fi kowa rauni a faɗin ƙasar nan.

Ahmed wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar NEMA a shiyyar Kudu maso Gabas, Ngozi Echeazu, ta ce an tantance gidaje 660,884 da aka yi niyya don cin gajiyar tallafin na musamman a faɗin jihohi 36 da babban birnin tarayya (FCT).

Ya ce an ba wa manoma kayayyakin amfanin gona irin su tsiron amfanin gona da kayan aiki, suna ba manoma damar koma wa gonakinsu, da ƙarfafa noman amfanin gona da kuma kare lafiyar abinci na ƙasa, ya ƙara da cewa, ana sa ran shiga tsakani zai zaburar da ayyukan sarƙaƙiya tun daga tushe.

KU KUMA KARANTA: NEMA ta ba da tallafin kayan agaji ga mutane dubu 23 a Nijar

Ya ci gaba da cewa, kayayyakin tallafin an yi su ne domin a taimaka wa masu sana’o’in hannu wajen inganta sana’arsu da bunƙasa tattalin arziƙinsu.

Ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da ka da su lalata kyakkyawar niyyar gwamnatin tarayya ta hanyar sayar da kayayyakin. Kayayyakin da aka raba sun haɗa da shinkafa, masara, dawa, ɗinki da injin niƙa.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, ta ce matakin abin a yaba ne matuƙa.

Wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma’aikata a ofishinta, Barista James Kanyip, ta ce; “Abin farin ciki a nan shi ne haɗin gwiwa tsakanin NEMA, SEMA da sauran hukumomi da gwamnatin jihar.

Hakan na nuni da cewa akwai alaƙa mai ƙarfi idan ana maganar magance bala’o’i da kuma samar da kayayyakin agaji ga waɗanda abin ya shafa ta irin wannan matakin.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *