Hukumar NDLEA ta shirya taron ƙarawa juna sani ga ɗaliban kiwon lafiya a Katsina

0
41
Hukumar NDLEA ta shirya taron ƙarawa juna sani ga ɗaliban kiwon lafiya a Katsina

Hukumar NDLEA ta shirya taron ƙarawa juna sani ga ɗaliban kiwon lafiya a Katsina

Daga Idris Umar, Zariya

A ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta gudanar da taron faɗakarwa na musamman ga ɗaliban kiwon lafiya na makarantar Khuddam da ke Ƙofar Ƙaura, Katsina.

Taron ya maida hankali ne kan wayar da ɗaliban game da illolin miyagun ƙwayoyi da tasirin su ga rayuwar matasa, tare da jan hankali kan yadda za a iya kaucewa amfani da su.

Muhammad Nura Salisu, jami’in hukumar NDLEA a jihar Katsina kuma mai kula da sashen koyarwa da faɗakarwa kan illolin kayan maye, ya gabatar da ƙasidar a madadin hukumar.

Ya yi bayani dalla-dalla game da illolin ƙwayoyi masu ƙarfi da na ruwa, da yadda suke lalata tunani da hankali.

KU KUMA KARANTA: 

Nura Salisu ya bayyana ire-iren miyagun ƙwayoyin da yadda suke illatarwa, tare da yadda ake gane masu ta’ammuli da su, da hanyoyin ba su shawara don dawowa hayyacinsu, daga matakin faɗakarwa har zuwa miƙa rahoton su ga hukumar don ta ɗauki mataki.

A cikin ƙasidar, ya yi bayani kan matakan da hukumar ke ɗauka na magance matsalolin masu tu’ammuli da ƙwayoyi, tun daga matakin ajewa a ba su masu shaye-shaye kulawa har zuwa matakin shari’a da hukunci ga manyan dillalai.

A zantawarsa da manema labarai, Nura Salisu ya ce sun zaɓi makarantar lafiya ta Khuddam don gudanar da wannan faɗakarwa duba da su malaman lafiya na iya amfani da ilimin su wajen taimakawa mutane kaucewa wannan yanayi ko samar da magungunan da ke da illa ga lafiyar ɗan’adam.

Ya ce ba makarantar Khuddam kawai ba, shirin zai ci gaba kamar yadda suka saba duk shekara na shiga lungu da saƙo na cikin al’umma don faɗakarwa da ƙara wayar da kan jama’a game da illolin ƙwayoyi da kuma bayyana matsayar hukumar NDLEA a kan masu tu’ammuli da ƙwayoyin.

Sunan shirin “War Against Drugs Abuse” (WADA), wanda duk inda suka gabatar da ƙasida suna duba ɗalibai masu hazaƙa don zama mambobin shirin don su taimakawa hukumar wajen wayar da kai kan illolin miyagun ƙwayoyi.

Taron da aka gudanar a dakin taro na makarantar Khuddam ya samu halartar malaman lafiya daga makarantar da wajen ta irin su Abdulmalik Ibrahim, Nuraddeen Garba, Aliyu Abba, Mr. Oka Okafor, Usman Hassan, Salisu Abdullahi, Madam Aisha, da Babangida Ibrahim, da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here