Hukumar NDLEA ta kama wata lauya da tarin miyagun ƙwayoyi

1
340

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta kama wata lauya mai suna Ebikpolade Helen, wacce ta ƙware wajen ƙera da rarraba skuchies, cakuɗa wiwi, opioids da black currant.

Wata sanarwa da kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce matar tana zaune ne a unguwar Lekki da ke Legas.

Mista Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani samame da aka kai garin Awka a jihar Anambara, biyo bayan kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5 da kwalabe 12 da aka shirya a baya a gidanta da ke Lekki.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA ta kama mutane 420 da ake zargi da sayar da miyagun ƙwayoyi a Kaduna

Ya kuma ce an kama wani wanda ake zargin Abubakar Shuaibu a ranar 13 ga watan Yuli a Cappa, titin Mushin-Oshodi ɗauke da kwalabe 86 na maganin tari na codeine.

Mista Babafemi ya ce magungunan da nauyinsu ya kai lita 8.6 suna cikin motar sa ƙirar Toyota Bus mai lamba FFA 241YB.

Kakakin hukumar ta NDLEA ya ce an kama mutane biyu Razak Ogunbo da Adeola Idowu a ranar 11 ga watan Yuli a Ikorodu ɗauke da lita 51 na skuchies.

Ya ƙara da cewa an gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 372 da kwalabe 48 masu nauyin lita 48 a gidan wani dillalin miyagun ƙwayoyi da ya gudu a Akala, Mushin Legas a ranar 12 ga watan Yuli.

“A jihar Ondo, jami’an tsaro sun aukawa wani gini da ke Ehin-Ala, ƙaramar hukumar Akure ta Kudu, inda suka kama wani Abubakar Zayanu Gyambar mai shekaru 28, ɗauke da buhunan skunk guda 162 da nauyinsu ya kai kilogiram 1,944.

“An kama wani wanda ake zargi, Henry Wilson, mai shekaru 50, a garin Ogume, Ndokwa West LGA, Delta, mai nauyin kilogiram 216.5,” inji shi.

1 COMMENT

Leave a Reply