Hukumar NDLEA ta kama ɗan kudancin ƙasar Amurka, ɗauke da hodar Iblis

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, ta kama wani matashi ɗan shekara 34 ɗan asalin ƙasar Suriname mai suna Dadda Lorenzo Harvy Albert da laifin safarar miyagun kwayoyi. NDLEA ta kama shi ne ɗauke da hodar Iblis mai nauyin kilogiram 9.9 da aka ɓoye a cikin kwaroron roba.

Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na NDLEA Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Mista Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne a filin jirgin sama na Fatakwal Port Harcourt International Airport) dake jihar Rivers, da laifin shigo da hodar iblis 117 cikin Najeriya. Ya ce an ɓoye magungunan ne a cikin kwaroron roba masu girma a cikin kwalabe na feshin jiki.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta sami lambar yabon rage shaye shayen miyagun ƙwayoyi a Borno

Ya kuma ce wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa ya bar ƙasarsa, Suriname, da ke gabar da tekun Arewa maso Gabashin Amurka ta Kudu a ranar 2 ga watan Afrilu zuwa Sao Paulo, ta Brazil.

Ya ƙara da cewa ya taso ne daga Sao Paulo zuwa Najeriya ranar Juma’a 7 ga watan Afrilu, a cikin jirgin ‘Qatar Airways’ domin neman mahaifinsa ɗan Najeriya da ya daɗe ba su haɗu, wanda ya ƙira da “Omini.”
Hakazalika, jami’an hukumar NDLEA a tashar jirgin ruwa ta Tincan da ke Legas sun kama wasu fakiti 110 na jihar Colorado.

Mista Babafemi ya ce an ɓoye nau’in tabar wiwi mai nauyin kilogiram 55 a cikin akwati mai lamba MSCU 4972769 daga Toronto ta hanyar Montreal, Canada. Ya ce an gano haramtattun kayan ne a cikin kwantenan da ke ɗauke da motocin da aka yi amfani da su guda biyar, yayin da hukumar NDLEA da masu ruwa da tsaki a tashar jiragen ruwa ta gudanar da gwajin haɗin gwiwa na kayan.

A halin da ake ciki, an kama wasu mutane biyu: Nura Ibrahim, mai shekaru 40, da Habibu Sadiq, mai shekaru 38, tare da Bulogi 120 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 148.7, a hanyar Zaria zuwa Kano a ranar Lahadi 2 ga watan Afrilu.

Mista Babafemi ya ce an gano ƙasa da kilogiram 418.5 na sinadari da wata motar safa ta sienna da aka yi amfani da ita wajen jigilar ta a ranar Alhamis, 6 ga Afrilu, a wata fitacciyar cibiyar shan magunguna, Patey, a birnin Legas.

“An kama wani da ake zargi, Azi Solomon, a ranar ɗaya ga wata a garejin Ojota a lokacin da yake ƙoƙarin ɗaukar tabar wiwi mai nauyin kilo 23 zuwa wata jiha,” in ji shi.


Comments

One response to “Hukumar NDLEA ta kama ɗan kudancin ƙasar Amurka, ɗauke da hodar Iblis”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA ta kama ɗan kudancin ƙasar Amurka, ɗauke da hodar Iblis […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *