Hukumar NDLEA ta kama ɗalibi ɗauke da miyagun ƙwayoyi mai nauyin gram 600

1
303

Hukumar yaƙi, hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta kama wasu ƙwayoyi guda biyu da suka haɗa da ƙwayar ‘skunk’ da za su je ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce jami’an NDLEA da ke da alaƙa da kamfanonin jigilar kayayyaki ne suka yi nasarar cafke kayan.

Mista Babafemi ya ce an ɓoye ƙwayoyin ne a cikin rigar aure kalar zinare, inda ya ƙara da cewa ƙwayar ‘skunk’ ɗin an ɓoye shi ne a cikin na’ura mai ƙwaƙwalwa. Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da aka kama wani ɗalibi mai karatun digiri na Injiniyan Ruwa a Jami’ar Neja-Delta, Amassoma, Jihar Bayelsa, Kelvin Ogenedoro, da laifin safarar gram 600 na ƙwayar skunk.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA ta kama kayan ƙwaya a cikin rigunan sanyi a Legas

Mista Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne a ƙofar jami’ar a wani samame da aka gudanar bayan kama kayan a cikin wata motar bas ta kasuwanci da ke kan titin Tombia zuwa Amassoma.

A wani labarin kuma, a jihar Adamawa, a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilu aka kama wani shahararren dillalin miyagun ƙwayoyi, Ishaku Emzor (Lalas) wanda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari a shekarar 2010 bisa laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Mista Babafemi ya ce an kama shi ne a Hayin Gada, ƙaramar hukumar Imburu Numan, inda ya je ya kai wa wani ɗan aikin ɓoye tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1.650.

“Barin sa na ‘Yellow Press Cub’ da ake amfani da shi wajen safarar miyagun ƙwayoyi an samu nasarar kama shi a wurin da aka kama shi.

“Haka zalika, an kama wani kuɗi N78,120 da ake zargin ana gudanar da wannan sana’ar ta haramtacciyar hanya daga hannun sa.

“A wannan rana a Kaduna, jami’an leƙen asiri sun kama wata babbar mota ɗauke da buhuna 110 da buhunan tabar wiwi 200 a Zariya.

“Magungunan suna da nauyin kilogiram 1,223 yayin da direban babbar mota, Adekunle Olanrewaju, mai shekaru 32, da mataimakinsa, Tunde Jamiu, mai shekaru 20, aka kama,” in ji shi.

1 COMMENT

Leave a Reply