Hukumar NDLEA ta fasa kamfanin ‘Akuskura’ a Adamawa

1
749

Hukumar yaƙi da da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta ƙona wata masana’anta a Adamawa dake kai wa ƙasashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar sinadarin Akuskura.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce an kai samame a kamfanin ne ranar Asabar a garin Mubi.

“A lokacin da aka kai farmakin, ana ci gaba da gudanar da ayyukan samar da kayayyaki a harabar,” in ji shi, ya ƙara da cewa an kama magunguna masu yawa.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA ta kama ɗalibi ɗauke da miyagun ƙwayoyi mai nauyin gram 600

Ya kuma ce jami’an hukumar a Binuwai sun ƙwato kwalaben ‘Syrup na Codeine’ guda 859 wanda nauyinsu ya kai kilogiram 117.3 da wani da ake zargin babban Dila ya yi watsi da su.

Kakakin NDLEA ya ce an yi watsi da kwalaben maganin tari mai nisan kilomita biyu daga wurin binciken hukumar NDLEA da ke kan hanyar Enugu zuwa Otukpo ranar Laraba.

Mista Babafemi ya kuma ce an kama wasu mutane biyu Kabiru Muhammed mai shekaru 35 da kuma Isah Muhammed mai shekaru 28 ɗauke da buhun tabar wiwi 20 mai nauyin kilogiram 11.2 da aka ɓoye a cikin buhun rogo (garri) a kan hanyar Zaria zuwa Kano ranar Juma’a.

A wani labarin kuma, jami’an tsaro sun ƙwato buhunan wiwi da bai kai kilogiram 74.5 ba a lokacin da suka kai samame a wani gini da ba a kammala ba a garin Ala da ke yankin Akure na jihar Ondo.

Mista Babafemi ya ce an gano kilo 60 na irin wannan abu da aka ɓoye a cikin takalmi a cikin buhu biyu na jumbo daga hannun wani Aminu Mohammed da ke kan hanyar Ibadan zuwa Oyo, jihar Oyo.

An kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake jiran ya hau mota zuwa Kebbi. Ya naƙalto shugaban hukumar ta NDLEA Buba Marwa yana yabawa jami’ai da mazan jiya a Kano, Ondo, Oyo, Benue da Adamawa bisa yadda suke taka-tsan-tsan da ƙwarewa wajen sauƙe nauyin da aka ɗora musu.

Mista Marwa ya tuhume su da takwarorinsu na faɗin ƙasar nan da ka da su huta a kan bakarsu.

1 COMMENT

Leave a Reply