Hukumar NDLEA a Kano ta kama mutane 49 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi

0
234
Hukumar NDLEA a Kano ta kama mutane 49 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumar NDLEA a Kano ta kama mutane 49 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) reshen Kano ta ce ta kama mutane 49 a cikin wani samame na kwanaki biyu da ta gudanar a ranar 7 da 8 ga watan Agusta, 2025.

An ce waɗanda aka kama na da alaka da laifuka daban-daban da suka shafi miyagun ƙwayoyi, tare da kwato kayayyaki da dama daga wajensu ciki har da tabar wiwi, magungunan Pregabalin da Diazepam, codeine, Rohypnol, “Suck and Die,” da makamai na gida.

Jaridar Neptune ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ASP Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar a madadin kwamandan rundunar, ACGN AI Ahmad.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama wani babban dilan ƙwaya a Kano

An gudanar da samamen ne a wuraren da aka dade ana zargin suna da alaƙa da miyagun ƙwayoyi, ciki har da Massallacin Idi, Fagge Plaza, Kofar Mata, Kofar Wambai, Kofar Dan’agundi, Makabartar Dan’agundi, Ladanai, Zage da Tashar Rimi a kasuwar Rimi.

Haka kuma, hukumar ta kai samame a tashar Kano Line da Tashar Rami da ke Na’ibawa, inda aka kama mutane fiye da 15.

Hukumar ta yi gargadin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kawar da miyagun ƙwayoyi daga cikin al’umma, tare da shawartar masu hannu a wannan haramtaccen aiki su daina kafin su fuskanci hukunci.

Sun ce suna ci gaba da bincike domin gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a gaban kotu.

Leave a Reply