Hukumar NAHCON ta sanar da kuɗin kujerar Hajjin 2025

0
23
Hukumar NAHCON ta sanar da kuɗin kujerar Hajjin 2025

Hukumar NAHCON ta sanar da kuɗin kujerar Hajjin 2025

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana Naira miliyan 8.3 da miliyan 8.4 da kuma miliyan 8.7 a matsayin ƙaranci da matsakaici da kuma mafi tsadar kuɗin kujerar aikin Hajjin da ke tafe.

Mataimakiyar Daraktar Yaɗa Labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta sanar cewa a maniyyatan da za su tashi ta jihohin Adamawa da Borno da Taraba da Yobe su ne za su biya mafi ƙarancin, Naira miliyan 8.327.

Maniyyatan sauran jihohin Arewa 15 da Babban Birnin Tarayya Abuja kuma za su biya Naira miliyan 8.457, a yayin da maniyyatan jihohin Kudu za su biya Naira miliyan 8.784.

KU KUMA KARANTA: NAHCON za ta haramta amfani da dala a aikin hajji, don rage tsadar kuɗin kujera

Fatima ta bayyana cewa Hukumar NAHCON, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Usman ta yi bakin kokarinta wajen ganin ba a ƙara kuɗin sosai daga abin da maniyyatan 2024 suka biya ba.

Ana samun bambancin kuɗin kujerar ne saboda bambancin nisan kowane yanki da Ƙasar Saudiyya.

Fatima Sanda Usara ta bayyana cewa Hukumar NAHCON ta sanar da kuɗin kujerar ne bayan samun sahalewar Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda hukumar ke ƙarƙashin kulawarsa.

Leave a Reply