Hukumar Kwastom ta kama waɗanda suka yi fasa-ƙwaurin sassan jikin wasu dabbobi

0
212
Hukumar Kwastom ta kama waɗanda suka yi fasa-ƙwaurin sassan jikin wasu dabbobi
Hukumar Kwastam a bakin aiki

Hukumar Kwastom ta kama waɗanda suka yi fasa-ƙwaurin sassan jikin wasu dabbobi

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Kano da Jigawa, ta kama wasu da ake zargi da fasa-ƙwaurin kilo 420 na kwanƙolin dabbar pangolin, waɗanda darajarsu ta kai miliyoyin naira.

Kwamandan Hukumar na shiyyar, Abubakar Dalhatu ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai, inda ya ce sumamen an kai shi ne a ranar 16 ga Yuli, 2025, ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Ofishin Kula da Dabbobin Jeji, Sashen Leƙen Asiri, da kuma Sashen ‘Yan Sanda na Hukumar Kwastam.

Ana farauta dabbar ne saboda naman ta da kuma kwanƙolin da ake amfani da su a magungunan gargajiya, musamman a ƙasashen Asiya.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Kwastam a Najeriya ta ƙwace tabar wiwi da ya kai Naira miliyan 117

Bincike ya nuna cewa fataucin kwanƙolin pangolin yana barazana matuƙa ga nau’in wannan dabbar a Najeriya, wanda hakan ke haifar da matsala ga daidaiton muhalli da nau’in halittu da ke rayuwa tare da ita.

Kwamanda Dalhatu ya ce an ƙaddamar da cikakken bincike domin gano wadanda ke da hannu a cikin wannan fatauci.

Ya kuma godewa Kwamanda-Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa bisa goyon bayan da suka bayar wajen tabbatar da nasarar wannan aiki.

Hukumar ta jaddada aniyar ta na ƙara sa ido ta amfani da fasahar zamani, domin hana fataucin dabbobi da kare nau’in halittu da ke fuskantar barazanar karewa.

Leave a Reply