Hukumar Kwastom reshen tashar jiragen ruwa na ‘Tin Can’ ta kama wasu tarin makamai da kayan soji da alburusai da kuma muggan ƙwayoyi da aka yi yunƙurin shigowa da su Najeriya ta ɓarauniyar hanya.
A wata sanarwa da hukumar ta kwastom ta fitar a juma’ar nan na cewa daga cikin muggan ƙwayoyin da aka kama sun haɗa da nauyin colorado da hodar iblis da kuma hodar koken.
A cewar kwanturolan kwastan mai kula da tashar jiragen ruwa ta Tin Can, Mr Dere Nnadi wasu jami’an hukumar ne suka gano inda aka ɓoye ƙwayoyin da makamai a wasu sunduƙai na kaya da aka yi yunƙurin shigo da su Najeriya.
Makaman da aka kama sun haɗa da bindigogi ƙirar ‘rifle’ masu sarrafa kansu da kansu.
KU KUMA KARANTA:Hukumar kwastam a Sokoto da Zamfara ta saki motoci 15 na hatsi da aka kama
Kuma yanzu haka dai hukumar ta kwastom ta ce tana tsare da wasu mutane da ke da alaƙa da haramtattun kayan da aka kama.
Najeriya ta daɗe tana fama da rashin tsaro wanda ya haifar da mutuwar mutane da dama a fiye da shekaru 10. Sau da yawa dai shugabanni da masu kula da harkokin tsaro na zargin ana shigowa da akasarin makaman ne daga ƙasashen ƙetare, abin da kuma ke ci gaba da ruruta wutar rikicin.
Mako guda da ya wuce kenan da ‘yan bindiga suka sace yaran makaranta kusan 300 a ƙauyen kuriga dake jihar kaduna.