Hukumar Kwastam a Najeriya ta ƙwace tabar wiwi da ya kai Naira miliyan 117

0
11
Hukumar Kwastam a Najeriya ta ƙwace tabar wiwi da ya kai Naira miliyan 117

Hukumar Kwastam a Najeriya ta ƙwace tabar wiwi da ya kai Naira miliyan 117

Hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa (NCS) reshen jihar Ogun, ta ƙwace tabar wiwi sativa da kuma allunan Tramadol waɗanda ƙuɗinsu ya kai naira miliyan 117.5 a kan iyakokin jihar Ogun.

Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a Abeokuta, Kwanturola James Ojo ya bayyana cewa jigilar ta haɗa da buhu 403, buhunan tabar wiwi 6,504, da fakitin allunan Tramakin 362 da aka ƙwace daga wasu wurare a ƙananan hukumomin Yewa ta Arewa da Imeko Afon Ojo ya yaba wa jami’an sa kan yadda suke taka-tsan-tsan, sannan ya gargaɗi masu fasa-kwauri da su daina ayyukan da ba su dace ba.

Kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Olusegun Adeyeye, ya karɓi haramtattun kayayyakin, inda ya yaba da haɗin kai tsakanin hukumar kwastam da NDLEA wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Da yake karbar baje kolin, Kwamandan NDLEA, Kwamandan Idiroko na musamman, Olusegun Adeyeye, ya yaba wa hukumar Kwastam kan rashin karewa, ƙoƙarin da gudunmawar da take bayarwa wajen yaki da miyagun ƙwayoyi.

KU KUMA KARANTA: Kwastam ta kama kwantainoni 12 ɗauke da kayan sojoji da miyagu ƙwayoyi

Adeyeye ya bayyana cewa, kwacen wata shaida ce da hukumar NDLEA da hukumar kwastam ke haɗa kai wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi.

Leave a Reply