Hukumar kula da birnin Abuja, ta gana da masana gine-gine

1
328

Hukumar da ke kula da babban birnin tarayya Abuja ta hannun sashen kula da ci gaban ƙasa ta gana da ƙwararru a fannin gine-gine domin magance matsalar rugujewar gine-gine da filaye da aka yi watsi da su.

Daraktan sashen kula da ci gaban ƙasa, Mukhtar Galadima, ya bayyanawa manema labarai a Abuja, ranar Laraba, cewa hukumar ta damu da kawo ƙarshen abubuwan da ke haifar da gini marar inganci.

Ya ce: “A matsayinmu na ƙungiyar da ke da haƙƙi, dole ne mu himmatu wajen tunkarar al’amurran da suka shafi rugujewar gine-gine, dole ne mu yi aiki tare da ƙwararrun hukumomi masu kula da hukumomi.

“Muna musayar ra’ayi kan yadda za a daƙile barazanar rugujewar gine-gine a babban birnin tarayya.

KU KUMA KARANTA: Jami’an birnin Abuja sun ruguza kasuwar dare

“Taron zai taimaka mana wajen kafa kwamitin da zai ba da shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalolin, ko da a baya amma a wannan karon za mu faɗaɗa shi.

“Za mu sanya shi ci gaba da kasancewa tare, tattaunawa da kulawa. Zai taimaka mana mu raba alhaki gami da ayyuka. ” Galadima ya bayyana cewa kwamitin da za a kafa nan ba da daɗewa ba zai kuma duba batutuwan da suka shafi gine-ginen da aka yi watsi da su da filaye da ba a gina su ba tare da samar da mafita.

Injiniya Cyril Nwafor, wanda ya wakilci Shugaban Majalisar Dokokin Injiniyoyi a Najeriya (COREN), ya buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa ta aiwatar da shawarwarin da aka aika wa majalisar a shekarar 2010.

Ya jera shawarwarin don haɗawa da shigar ƙwararrun masu rajista kawai don gudanar da ayyukan da kuma ladabtar da waɗanda ke bayan ayyukan da suka gaza.

Sauran ƙwararrun hukumomin da suka halarci taron sun haɗa da Architect Registration Council of Nigeria (ARCON), Council of Registered Builders of Nigeria (CORBON) da dai sauransu.

1 COMMENT

Leave a Reply