Hukumar kiyaye haɗurra ta FRSC, ta koka da yawaitar tudun taƙaita gudu akan hanyar Gombe zuwa Yola

2
350

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta koka kan yawaitar tudun taƙaita gudu ‘bump’ ‘ba bisa ƙa’ida ba a babbar hanyar Gombe zuwa Yola.

Babban kwamandan hukumar FRSC a jihar Gombe Felix Theman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya laraba.

A cewarsa, abin rage gudun ba kawai suna haifar da babban haɗari ga jama’a masu ababen hawa ba, har ma suna haifar da lalata hanyar da wuri wanda gwamnati ke kashe kuɗi wajen ginawa.

Ya ce tsakanin al’ummomin Cham da Bambam da ke kan babbar hanyar da ta ke da nisan kilomita 40, al’ummomi sun kafa ‘bump’ kusan tudu 57 ba gaira ba dalili, ya ƙara da cewa akwai kuma wasu 18 a kan hanyar Bambam zuwa garin Kaltungo. “

KU KUMA KARANTA: Jami’an hukumar FRSC za su fara kama motocin da lambarsu suka shuɗe

Direbobi sun ka sa bin ƙa’idojin gudu a wuraren da aka gina, al’ummomi kuma ba su bari hanyoyin su kasance ba yadda suke ba.

Yakamata al’umma su nisanta kansu daga wannan aikin ta taimakon kai domin yin hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba kawai amma a ƙarshe zai haifar da lalacewar hanyar da al’umma ke matuƙar buƙata.

“Ya kamata al’ummomi su yi ƙira ga mai kula da ayyuka na tarayya wanda alhakinsa shi ne kimanta matsalolin tsaro da nufin samar da mafita mafi aminci kamar yadda ya dace,” in ji kwamandan.

Ya kuma bayyana cewa aƙalla mutane bakwai ne suka mutu sannan 20 suka samu raunuka sakamakon haɗurra mota da aka yi a lokacin bikin ƙaramar Sallah da aka yi a jihar Gombe inda ya buƙaci masu ababen hawa da su riƙa tuƙa mota a ƙa’idance.

2 COMMENTS

Leave a Reply