Hukumar kashe gobara a Kano, ta tabbatar da mutuwar wani mutum a yayin ɗebo ruwa a rafi

0
351
Hukumar kashe gobara a Kano, ta tabbatar da mutuwar wani mutum a yayin ɗebo ruwa a rafi

 

Hukumar kashe gobara a Kano, ta tabbatar da mutuwar wani mutum a yayin ɗebo ruwa a rafi

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wani mutum mai shekaru 30, mai suna Rabiu Sani a garin Kunture, karamar hukumar Ungogo ta Jihar Kano , ya rasa ransa bayan ya zame ya fada cikin wani rafi lokacin da ya je ɗebo ruwa.

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:57 na safe daga wani ɗan sanda mai suna Silas Munkhaila, wanda ya sanar da ita game da lamarin.

Nan take tawagar ceto ta shirya kuma ta isa wurin da misalin ƙarfe 10:15 na safiyar ranar Asabar, a cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara, ACFO Saminu Yusif Abdullahi.

Abdullahi ya ce mahaifin mamacin ne ya tura shi don ya debo masa ruwa sai ya zame ya fada cikin ruwan kuma ya kasa fitowa.

KU KUMA KARANTA:Barau Jibrin ya fi Ganduje hannu a haddasa rikicin siyasar Kano – Jaafar Jaafar

Ya ce ƙoƙarin tawagar na ceton rayuwar maximum ya ci tura inda aka tabbatar da mutuwarsa a wurin.

Abdullahi ya ce an mika gawar mamacin ga dagacin garin Kunture, Uba Abdulkadir, inda daga nan za a mika shi ga iyayen sa domin yi masa suttura.

Hukumar kashe gobara ta yi kira ga mazauna gari da su yi taka-tsantsan yayin amfani da wuraren da ake debo ruwa don guje wa faruwar irin wannan haɗari.

Leave a Reply