Hukumar Hisbah a Kano, ta kama mutane 62 da ake zargi da baɗala a Dawakin Kudu 

0
268
Hukumar Hisbah a Kano, ta kama mutane 62 da ake zargi da baɗala a Dawakin Kudu 

Hukumar Hisbah a Kano, ta kama mutane 62 da ake zargi da baɗala a Dawakin Kudu

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama maza 27 da ƴan mata 35 da ake zargi da aikata badala a makarantar NITT da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Kano.

Hisbah ta bayyana cewa, jami’anta sun kai samame wurin a ranar Lahadin nan bayan samun bayanan sirri da ƙorafe-ƙorafe.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Hisbah a Yobe ta kama kwalaben giya, ta rufe gidajen Karuwai a Gashuwa

Jamiʼan Hisbar sun ce, sun tarar da waɗanda ake zargin suna gudanar da taro da ake alakantawa da ayyukan badala.

Tuni aka taho da su ofishin hukumar domin ci gaba da bincike, kafin ɗaukar mataki na gaba.

Leave a Reply