Hukumar Hisbah a Kano ta kama matasan da ba sa yin azumi da masu aikin banza

0
5

Hukumar Hisbah a Kano ta kama matasan da ba sa yin azumi da masu aikin banza

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Jami’an Hukumar Hisba a jihar Kano sun kama wasu matasa gandaye da ake zargi da kin yin azumi a ranar farko ta watan Ramadan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Aminuddeen ne ya tabbatar da kamen ga manema labarai a jihar.

Ya kara da cewa an kama matasan ne yayin sintiri da jami’an hukumar ke yi a sassa daban-daban na birnin Kano.

Haka kuma, hukumar ta cafke kimanin mutane 60 da ke da askin banza, wanda ya sabawa dokokin shari’a da al’adun gari.

Bugu da kari, Hisba ta kama wasu direbobin baburan adaidaita sahu (keke napep) da ake zargi da cakuda maza da mata a baburansu, lamarin da hukumar tace ba za ta lamunta da shi ba.

Hukumar ta Hisba ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da sintiri don tabbatar da bin dokokin shari’a a cikin watan Ramadan.

Leave a Reply