Hukumar FIFA ta dakatar da Samuel Eto’o, Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru

0
55
Hukumar FIFA ta dakatar da Samuel Eto'o, Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru

Hukumar FIFA ta dakatar da Samuel Eto’o, Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA ta dakatar da Samuel Eto’o, shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru tsawon watannin shida, sakamakon karya dokar da ta shafi muzanta mu’amala da rashin ɗa’a.

Kwamitin ladabtarwa na FIFA ya fitar da sanarwa mai cewa, “Kwamitin Ɗa’a na FIFA ya hukunta shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Kamaru, (FECAFOOT), Samuel Eto’o, da wa’adin dakatarwa ta wata shida, daga halartar wasanni a matsayin wakilin Kamaru.

Kwamitin ladabtarwa na FIFA ya fitar da sanarwa mai cewa, “Kwamitin Ɗa’a n FIFA ya hukunta shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru, (FECAFOOT), Samuel Eto’o, da wa’adin dakatarwa daga halartar wasannin tawagogin Kamaru tsawon wata shida.

An ladabtar da Eto’o ne saboda keta saɗarar doka ta 13 (muzanta mu’amala da saɓa dokar daidaito a wasanni) da ta 14 (Rashin ɗa’ar ‘yan wasa da jami’an wasa) kan Dokar Ladabtarwa ta FIFA.

Sanarwar ta ce, “AN yi wannan hukunci ne saboda wasan da aka buda a gasar Kofin Duniya ta Mata ‘yan ƙasa da shekara-20, a wani wasa tsakanin kamaru da Brazil, zagaye na ‘yan 16, tsakanin Brazil da Kamaru wanda aka buga a Bogotá, Colombia, ranar 11 ga Satumban 2024.

KU KUMA KARANTA: Da wane dalili PDP ta dakatar da Dino Melaye?

Haramcin kan Mr Eto’o zai hana shi halartar wasannin tawagogin maza ko na mata na hukumar FECAFOOT, cikin dukkan rukunai da matakan shekaru. An sanar da Mr Eto’o yau game da ranar da haramcin zai fara aiki.”

Wannan dakatarwa da aka yi wa Eto’o ba shi ne karo na farko da ake jin sunansa kan batun halayya mara kyau.

Tsohon ɗan wasan da ya taka leda Barcelona da Chelsea, a baya an zarge shi da yin barazana ga ‘yan wasa da kocin Kamaru, Marc Brys, kuma ya ci zarafin wani masoyin ƙwallo a waje n filin wasa lokacin gasar Kofin Ƙwallon Ƙafa na Duniya a Qatar 2022.

Ba a san ko Eto’o zai komo kan aikinsa ba bayan cikar wa’adin dakatarwar ta wata shida. Ko ma mene, halayyarsa tana shafar mutuncin ƙasarsa a fagen wasan ƙwallo.

Leave a Reply