Hukumar FCCPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 220 a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cin tarar kamfanin Meta tarar dala miliyan 220, inda ta ce binciken da ta gudanar ya gano an saɓa dokokin kare bayanai na ƙasar lokuta da yawa a shafukan Facebook da WhatsApp.
A wata sanarwa da Hukumar kare haƙƙoƙin masu sayayya ta FCCPC ta fitar, ta lissafa hanyoyi biyar da kamfanin Meta ya saɓa dokokin bayanai a ƙasar da ke yammacin Afirka, ciki har da ta hanyar musayar bayanan ‘yan Najeriya ba tare da izininsu ba, nuna wariya da sauransu.
Nan take dai mai magana da yawun kamfanin Meta bai maida martini kan buƙatar yin bayani a kan batun ba.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarar kamfanin Facebook tana neman ya biya tarar N30bn
Najeriya, ƙasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka, ta na da manyan rukunonin da aka fi amfani da intanet a duniya inda mutane miliyan 154 suka yi rijistar amfani da intanet a shekarar 2022, a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasar.
Duk da yawan masu amfani da intanet a ƙasar, kamfanin Meta ya ka sa bin dokokin kariyar bayanai ta Najeriya.
Bayan tarar dala miliyan 220, umurnin hukumar ya buƙaci kamfanin Meta ya kiyaye dokokin cikin gida na Najeriya ya kuma daina “ci da gumin ‘yan Najeriya masu amfani da shafukan.
A watan Mayun shekarar 2021 ne aka fara binciken saɓa ƙa’idodjin a lokacin da hukumar ta buɗe wani bincike kan wasu sabbin manufofin amfani da shafin WhatsApp. Ta kuma sanar da kamfanin Meta sakamakon binciken, lamarin da ya sa daga baya kamfanin ya gabatar da ƙudurin yin garambawul wanda ya ka sa magance matsalolin farko, a cewar sanarwar.