No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar DSS ta kama shugaban NLC, Ajaero

Hukumar Tsaro ta DSS ta kama Shugaban Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC), Kwamred Joe Ajaero.

Da sanyin safiyar Litinin jami’an DSS suka yi awon gaba da Kwamred Ajaero a filin jirgin sama da ke Abuja.

DSS ta kama Ajaero ne a hanyarsa ta zuwa ƙasar Birtaniya, inda zai halarci Babban Taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya, wanda za a fara ranar Litinin ɗin a birnin London.

KU KUMA KARANTA: Za mu shiga yajin aiki matuƙar wani abu ya sami shugabanmu – NLC

Majiyoyin tsaro a hedikwatar DSS da ke Abuja sun tabbatar wa Aminiya cewa Ajaero na hannunsu, sun titsiye shi da tambayoyi.

Wata majiya ta shaida mana cewa tsare Kwamred Ajaero na da nasaba da zargi da ake masa na dauƙar nauyin ta’addanci.

Ana iya tuna cewa a kwanakin baya, ’yan sanda sun tsare Kwamred Ajaero tare yi masa tambayoyi bayan sum zarge shi da hannu a ɗaukar nauyin ta’addanci.

A ranar 29 ga watan Agusta ’yan sanda suka yi masa tambayoyi a Abuja, daga bisani suka sallame shi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...