Hukumar Alhazan Najeriya ta fitar da sabon kuɗin aikin Hajjin bana

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta fitar da sabon kuɗin kujerar aikin Hajjin 2024.

A kwanakin baya ne dai hukumar ta saka naira miliyan huɗu da dubu ɗari biyar a matsayin kafin alƙalami, sai dai a sanarwar da ta fitar ta ce ta yi niyyar barin wannan kuɗin a matsayin kuɗin Hajji amma hakan ba zai yiwu ba sakamakon karyewar darajar naira.

A halin yanzu hukumar ta ce maniyyata daga kudancin Najeriya za su biya N4,899,000 a matsayin kuɗin aikin Hajji sai kuma waɗanda suka fito daga arewacin ƙasar za su biya N4,699,000, sai kuma waɗanda suka fito daga jihohin Yola da Maiduguri su biya N4,679,000.

KU KUMA KARANTA: NAHCON ta sanar da yadda Saudiyya ta rage kuɗin aikin Hajjin bana

A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, ta bayyana cewa hukumar ta bayar da shawara ga maniyyata su biya sauran kuɗin da ya rage na Aikin Hajjin zuwa Litinin 12 ga watan Fabrairu domin bai wa hukumar damar tura kuɗaɗen Aikin Hajjin.

Wannan ƙarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar karyewar darajar naira a Najeriya, lamarin da ya jawo matsin tattalin arziki a ƙasar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *