Sabon Shugaban hukumar alhazai ta Jihar Kaduna, Salihu Abubakar, ya roƙi limamai su taimaka wajen wayar da kan maniyyata su ƙoƙarta cika kuɗin kujera Hajji bana kafin ranar 31 ga watan nan Disamba da muke ciki.
Malam Salihu ya ce akwai buƙatar a tuna wa maniyyata cewa har yanzu ana karɓar kuɗin kujera, saboda nan da ’yan kwanaki za a rufe karɓar kuɗin kujera da aka nemi duk maniyyaci ya biya naira miliyan 4 da rabi.
Ya Kuma shawarci maniyyata da su tabbatar da sun karɓi takardun bankin a ofishoshin Hukumar dake a ƙananan hukumomi 23 a jihar domin zuwa su biya kuɗin kujerarsu.
“Muna tabbatar wa maniyyata cewa za mu tabbatar da an rike masu amanar dukiyarsu kuma har yanzu ana ci gaba da karɓar kuɗin kujerar har zuwa ranar 31 ga watan nan na Disamba” in ji shi.
KU KUMA KARANTA: NAHCON ta ba maniyyata aikin hajjin baɗi mako uku su fara biyan kuɗaɗensu
Ya ce ana buƙatar Hukumar Alhazan ta miƙa kuɗaɗen waɗanda suka biya kujerarsu ga Hukumar Aikih Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a ranar 5 ga watan Janairu 2024, kamar yadda dokar Hukumar ta tanadar, shi yasa ake ƙira ga sauran maniyyata da su ƙoƙarta su kammala cikan kuɗinsu.