No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sabon Shugaban hukumar alhazai ta Jihar Kaduna, Salihu Abubakar, ya roƙi limamai su taimaka wajen wayar da kan maniyyata su ƙoƙarta cika kuɗin kujera Hajji bana kafin ranar 31 ga watan nan Disamba da muke ciki.

Malam Salihu  ya ce akwai buƙatar a tuna wa maniyyata cewa har yanzu ana karɓar kuɗin kujera, saboda nan da ’yan kwanaki za a rufe karɓar kuɗin kujera da aka nemi duk maniyyaci ya biya naira miliyan 4 da rabi.

Ya Kuma shawarci maniyyata da su tabbatar da sun karɓi takardun bankin a ofishoshin Hukumar dake a ƙananan hukumomi 23 a jihar domin zuwa su biya kuɗin kujerarsu.

“Muna tabbatar wa maniyyata cewa za mu tabbatar da an rike masu amanar dukiyarsu kuma har yanzu ana ci gaba da karɓar kuɗin kujerar har zuwa ranar 31 ga watan nan na Disamba” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: NAHCON ta ba maniyyata aikin hajjin baɗi mako uku su fara biyan kuɗaɗensu

Ya ce ana buƙatar Hukumar Alhazan ta miƙa kuɗaɗen waɗanda suka biya kujerarsu ga Hukumar Aikih Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a ranar 5 ga watan Janairu 2024, kamar yadda dokar Hukumar ta tanadar, shi yasa ake ƙira ga sauran maniyyata da su ƙoƙarta su kammala cikan kuɗinsu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...