Hukumar alhazai ta Adamawa ta buƙaci maniyyata su fara ajiye Naira miliyan 8

0
82
Hukumar alhazai ta Adamawa ta buƙaci maniyyata su fara ajiye Naira miliyan 8

Hukumar alhazai ta Adamawa ta buƙaci maniyyata su fara ajiye Naira miliyan 8

Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Adamawa, Malam Abubakar Salihu ya ƙira wani taron gaggawa da jami’an aikin Hajji na ƙananan hukumomi a jihar.

A wata sanarwa da sashen yaɗa labarai na hukumar ya aike wa Hajji Reporters Hausa, Salihu ya ƙira taron ne kan tsare-tsaren jadawalin shirye-shiryen aikin Hajjin baɗi.

A yayin ganawar, Malam Salihu ya yi jawabi a kan batutuwa da dama, inda mafi fice a cikin su shi ne kuɗin aikin Hajjin 2025.

KU KUMA KARANTA:Hajji 2025: Saudiyya za ta hana masu matsananciyar jinya zuwa aikin Hajji

A cewar sanarwar, shugaban hukumar ya yi ƙira ga maniyyata daga jihar da su je banki su fara ajiye Naira miliyan 8.2 na kuɗin aikin Hajjin kafin hukumar alhazai ta ƙasa ta yanke cikakken farashin aikin hajji na shekara mai zuwa.

Ya kuma umarci jami’an hajji da su fara aikin rijistar maniyyata a kananan hukumomin da su ke aiki.

Leave a Reply