Hotunan tauraron ɗan’adam na MƊD sun tabbatar da lalata kashi 35 na gine-ginen Gaza

0
121

Hotunan tauraron ɗan’adam da cibiyar tauraron ɗan’adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi nazari sun nuna cewa kashi 35 cikin 100 na gine-ginen Gaza sun lalace sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa yankin Falasɗinawa.

Hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar a matsayin mayar da martani ga hare-haren Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa kusan 32,000, a cewar hukumomin lafiya a Gaza.

A cikin tantancewar da ta yi, Cibiyar Tauraron Dan’Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNOSAT, ta yi amfani da hotuna na tauraron ɗan’adam da aka tattara a ranar 29 ga watan Fabrairu tare da kwatanta su da hotunan da aka dauka kafin da bayan fara sabon rikici.

KU KUMA KARANTA: Taron ƙungiyar AU na nemo hanyar warware matsalolin da ke addabar nahiyar Afirka

An gano cewa kashi 35 cikin 100 na dukkan gine-gine a Gaza — gine-gine 88,868 – sun rushe ko kuma sun lalace.

Daga cikin waɗannan, ta gano gine-gine 31,198 da aka lalata, 16,908 sun rushe baki ɗaya, sannan 40,762 sun lalace sosai.

Leave a Reply