Hotunan Falasɗinawa mata da matasa da Hamas ta sa aka saki daga kurkukun Isra’ila

0
228

Falasɗinawa a faɗin Gabar Yammacin Kogin Jordan sun yi ta sowa da daga tutocin Falasɗinu da na Hamas da kuma maratayin kaffiyeh bayan Isra’ila ta saki Falasɗinawa 39 da take tsare da su shekara da shekaru.

“Ina cike da farin cikin amma ‘yancina ya samu ne bayan mutane da dama sun yi shahada,” in ji Marah Bakir, mai shekara 24, inda take magana a kan kusan mutum 15,000 da Isra’ila ta kashe a Gaza tun lokacin da ta ƙaddamar da hare-hare.

Hanan al Barghouti, mai shekara 58, wadda aka saka daga kurkukun Isra’ila bayan ta kwashe wata biyu, ta jinjina wa Hamas da shugabanninta da al’ummar Gaza.

Ta yi addu’ar “Allah ya saka musu da alheri. Idan ba domin al’ummar Gaza suke aiki ba da ba za mu samu ‘yanci ba. “Muna cikin kurkuku muna shan ukuba. Matsiyata ne. Sun ci zarafinmu, sun wulakanta mu. Amma hakan bai sa mun sarayar da mutuncinmu ba, kuma muna godiya bisa wannan jajircewa da aka yi.”

Ga hotunan wasu daga cikin mata da matasa da aka saka daga gidajen yarin Isra’ila.

Leave a Reply