Hukumar Hisbah ta yi nasarar kama wasu mutane da suke cin kasuwar mushen rago da kaji haɗi dayin balangunsa.
Kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Tarauni malam Nasir Adam Mai kaji yace dakarun Hisbah na ƙaramar hukumar Tarauni ne su kayi nasarar kamo mutanen a daidai lokacin da suke yunkurin tafiya da naman mushen domin kaiwa kasuwa.
Kwamandan ya ce abin da takaici yadda mutanen da suke iƙirarin su musulmi ne a ce suna ɗaukar mushe a bola su gyara da nufin sayarwa mutane wanda yin hakan ka iya jawo cutuka ga mutane waɗanda ba za’a iya gane kansu ba.
KU KUMA KARANTA: Hisbah ta cafke mutum 37 kan karuwanci da sayar da giya a Yobe
Yayi ƙira ga al’umma da su himmatu wajen kai mushen dabbobinsu gidan kula da namun daji ko kuma su binne shi domin kaucewa ɓata gari kofar siyar da mushe ga al’umma.
Mutanen da aka kama Aminu Abdullahi da Isyaku Musa sun tabbas suna sayar da mushen ne a sabon gari, kuma masu amfani da mushen sukan basu kyautar barasa tare da biyansu kuɗaɗe.
Sai dai Aminu da isyaku sun ce sun yi nadamar rungumar wannan sana’ar da suka ɗauki tsawon lokaci suna gudanarwa ba tare da an kamasu ba, sai a wannan karon sun kuma yi alwashin daina wannan sana’ar kwata kwata.
A nasu ɓangaren hukumar Hisbar ta umarci mutanen biyu su binne naman duk da wani balangun mushen da sukayi duk da sun bayyana cewa suma su na cin balangun da sukayi da mushen.