No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kebbi sun kama wani mutum mai suna Muhammad Ɗahiru, mai shekaru 33 bisa zargin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a Birnin-kebbi.

Hisbah ta bayyana a shafinta na Facebook cewa wanda aka kama ya ɗauki yarinyar a kabu-kabu daga nan sai ya zarce da ita zuwa cikin daji inda ya yi mata fyaɗe.

An kama Ɗahiru ɗan karamar hukumar Koko/Besse a jihar a ranar Litinin, 11 ga Disamba, 2023.

Ɗahiru ya amsa laifinsa kuma an miƙa shi ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi gaban ƙuliya.

KU KUMA KARANTA: Za a fara dandaƙe masu yin fyaɗe a Kaduna

Nafiu Zaki, shugaban ƙungiyar ‘yan acaba na jihar Kebbi ya ce basu da masaaniya game da lamarin balle su iya tabbatar da sahihancin wanda aka kama ko ainihin ɗan ƙungiyar ‘yan acaba na jihar Kebbi ne ko akasin haka kawo lokacin rubuta wannan rahotu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...