Hisbah ta fara kwashe yara da ke gararamba a tituna

0
32
Hisbah ta fara kwashe yara da ke gararamba a tituna

Hisbah ta fara kwashe yara da ke gararamba a tituna

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin jihar Kano, ta hannun hukumar Hisbah ta fara kwashe ƙananan yara da ke gararamba a tituna a faɗin birnin jihar.

A hira da manema labarai a ranar Talata, shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce a halin yanzu hukumar ta kama yara 220.

A cewar sa, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya sahale wa hukumar da ta kwashe yaran, wanda ya ce shekarun su sun fara daga 18 zuwa 10.

Hisbah ta fara kwashe yara da ke gararamba a tituna

 

A cewar Malam Daurawa, an kama yaran ne a gurare daban-daban da su ka haɗa da bakin tituna, ƙarƙashin gadoji, tashoshin mota da sauransu.

Ya ƙara da cewa a cikin yaran da aka kama, an gano yan ƙasar Nijar 11, sai kuma “na Kano 86, Katsina 44, Jigawa 16, Gombe 3, Neja 4, Bauchi 7, Yobe 8, Kaduna 18, Kebbi 2, Sokoto 3, Nassarawa 1, Zamfara 10, sai kuma na jihar Adamawa 1.

KU KUMA KARANTA: Kar a wuce ƙarfe 11 na dare a wuraren taron buki a Kano  Hukumar Hisbah

“Kafin su zo, mun yi tanadi mun yi shiri kuma a cikin kwamitin da Mai Girma Gwamna ya kafa akwai kwamishinoni 3. Mun kamo yaran nan ne a aikin da mu ka fara yi tsakar dare inda mu ka bi wuraren kwanciyar su,”

“Duk wannan da nufin samar musu rayuwa mai kyau daga cire su daga rayuwar ƙasƙanci,” in ji shi.

Yanzu haka an ajiye yaran a sansanin alhazai na jihar Kano inda ake ci da su da shayar da su da kuma basu karatu.

Leave a Reply