Hisbah a Katsina za ta fara kamen mabarata

Hukumar Hisbah za ta fara kamen masu bara a faɗin ƙananan hukumomi 34 da ke Jihar Katsina.

Babban Kwamandan Hisbah na jihar, Dokta Aminu Usman (Abu-Ammar), ya ce hukumar za ta kori duk mabarata da ba ’yan asalin jihar ba ne zuwa jihohinsu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana jaddada aniyar hukumar Hisbah ta kawar da mabarata daga titunan jihar.

Dokta Aminu Usman ya ce, “gwamantin Katsina na yin duk mai yiwuwa don kawar da bara a titunan jihar, saboda bara ba ta daga cikin addinmu, sai dai ma zubar da kimar addininmu da al’ummarmu da take yi.

“Dokar da ta kafa hukumar Hisbah ta ba mu ikon bin lungu da sako mu tantance mabarata, mu gano mabuƙata na ainihi a cikinsu, mu miƙa su ga Hukumar Zakka da Wakafi domin ta tallafa musu,” in ji shi.

Shugaban na Hisbah ya ce gwamnatin jihar ta kafa hukumar Zakka da Waƙafi ne musamman domin tallafa wa mabuƙata.

Abu-Ammar ya ce wadanda ba ’yan asalin Jihar Katsina ba ne daga cikin waɗanda aka gano kuma za a mayar da su johohinsu.

Sannan ya ce, hukumar Hisbah a shirye take ta yi maganin masu baɗala da rashin tarbiyya a jihar, don haka ya buƙaci iyaye da sauran jama’a su rika kula da tarbiyyar ’ya’yansu.

Ya ce gwamnatin jihar ba za ta ƙara lamuntar rashin tarbiyya ba a tsakanin matasa, don haka duk wanda aka kama saboda baɗala, zai yaba wa aya zaƙi a hannun hukumomin da suka dace.

KU KUMA KARANTA: Hisbah a jihar Kebbi ta sami ƙananan yara ‘yan mata su biyu suna gararamba a gari

Babban Kwamandan Hisban ya ce waɗanda aka kama da ba ’yan jihar Katsina ba ne kuma, za a damƙa su a hannun hukumomin da suka dace a jihohinsu.

“Babu mahaifin da zai so ganin matashi na shaye-shaye da sauransu, don haka muke ƙira ga iyaye da sarakunan gargajiya da sauran jama’a su ba mu goyon baya da haɗin kai wajen cimma manufar nan ta kyautata rayuwar matasanmu,” in ji shi.

Daga nan sai ya roƙi al’umma da su rika fallasa ɓata-gari da wuraren aikata baɗala da ke yankunansu domin a ɗauki matakin da ya dace.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *