Hisbah a jihar Kebbi ta sami ƙananan yara ‘yan mata su biyu suna gararamba a gari

Jami’an hukumar Hisbah na jihar Kebbi sun sami ‘yan mata yara ƙanana guda biyu suna gararamba a garin Birnin kebbi.

Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da hukumar ta wallafa ranar Asabar 23 ga watan Disamba 2023.

Sanarwar na ɗauke da cewa:

“ANSAMU ƘANANAN YARA MATA SU BIYU SUNA GARARANBA A BIRNIN KEBBI

Hukumar Hisbah ta samu Yara ‘yan mata guda biyu, ɗaya mai suna Aisha lawali jah ‘yar ƙauyen magazu unguwar sabon layi dake tsafe local govt zamfara state.

KU KUMA KARANTA: Hisbah ta kama ɗan acaɓa da ya yi wa yar shekara 12 fyaɗe

Sai ɗayar kuma mai suna Nasmatu Abdullahi gwangwala, ‘yar ƙauyen kunduttu dake maiyama local govt jihar kebbi 

Duk kansu sun zo yawo ragaita ne garin Birnin Kebbi. Hukumar Hisbah ta jihar kebbi ta zanta da hukumar Hisbah ta zamfara don gano iyayen Aisha magazu don sadata dasu.

Haka ma hisbah ta zanta da kakan Nasmatu dake ƙauyen unguwar kurya ta maiyama shikuma yana cikin yanayin rashin lafiya da bazai iya zowa ba don tace babanta ya rasu mamarta na aure barkeji ta jihar sokoto

Allah ya shiryadda zuriar mu yayi muna tsari ameen”.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *